’Yan kungiyar ta Da’ish sun dade suna barazanar karbe Ramadi, bayan sun ta kai farmaki a yankin inda suke haduwa da turjiya ta sojin kwamnati.
Rahotanni sun ce ’yan ta’addan sun karbe babbar hedikwatar gwamnati da misalin karfe 2 na rana tare da kafa tutarsu.
Kamfanin dillacin labaran Faransa ya ruwaito cewa mutanen yankin na ficewa garin da kafa ba tare da dukiyoyinsu ba.
Majiyoyin tsaro sun ce ‘yan ta’addan sun karbe ikon garuruwa da suka kewaye Ramadi a lardin Anbar tare da sadaukar da nasarar da suka samu ga Abu Muhannad al-Swaidawi babban kwamandan kungiyar da ke kula da lardin.ABNA